Bayanai daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, tare da sace ɗalibai waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Lamarin dai ya faru ne da asubahin ranar Juma’a, inda rahotanni ke cewa maharan sun kutsa gidajen kwanan ɗalibai guda uku a unguwar Sabon Gida da ke mawaftaka da jami’ar.
Bayanan na cewa ƴan bindigar sun samu nasarar kwashe kusan dukkanin ɗaliban da ke zaune a gidajen waɗanda ke daura da jami’ar.
Har yanzu dai hukumomi ba su yi ƙarin bayani kan lamarin ba.
Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi jigata daga ayyukan ƴan bindiga masu fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Ko a cikin watan Fabarairun 2021, ƴan bindiga sun shiga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a jihar, inda suka sace ɗalibai mata 317.
Haka nan ma a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.
Maharan sun abka ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako da rana tsaka, inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkiɗa tare da jikkata karin wasu.
Ita dai gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal, ta ce tana ɗaukar duk matakan da suka dace wajen shawo kan lamarin, sai dai ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba.
A baya dai gwamnatocin da suka gabata a jihar sun ɗauki matakai daban-daban, ciki har da na yarjejeniya da ƴan bindigar, sai dai har yanzu matsalar ta ci tura.
BBC Hausa