Sakon Abba Kyari daga Baki mai Dakinsa bayan taje ta fada masa ibtila’i daya faru a kasuwan Monday Market dake Maiduguri.
Nayi Matukar Bakin Ciki, yayin da wannan mummunar Labari ya iske ni.
Ina mika Sakon jaje ga ilahirin mutanen Maiduguri da Al’umar Borno da kewaye dakuma Yan Kasuwa, da kuma Yan uwa da abokanen Arziki bisa wannan mummuinar ibtil’i da ya faru na gobara da ya kone miliyoyin dukiyoyi da kadorori.
Ina rokon Allah, daya kawo muku sauki ta kowanne Hanya da zai Sa ku farfado ku koma kasuwanchi ku fiye da na da In Shaa Allah.
A Gaskiya, bazan iya kwatanta irin asara da aka yi a wananna mummunar Alamarinba. Allah ne kawai zai iya biyanku.
Ina kara mika sako Jaje na ga ilahirin jama’ar Maiduguri, da duk Borno state, Yan Kasuwa, Abokanen Arziki da dukkanin mutane da wannan abun ya shafesu.
Allah ya sa Mudace, Allah ka taimeke mutanen da sukayi Asara, Allah ka taga su fiye da Na da, Amin Amin Amin.