Yadda sojojin Najeriya suka yi wa yanbindiga ruwan wuta

Posted admin Arewa & Kai News 118 Views 2 Min Read
2 Min Read

 

Rundunar sojan saman Najeriya ta ce ta yi wa ayarin wasu ‘yanbindiga ruwan wuta da ke kan babura goma sha biyar a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Rundunar ta ce kowane abinhawa yana dauke da aƙalla mutum biyu, kuma ta ce ta yi nasarar halaka su, kamar yadda daraktan hulda da jama’a da sadarwa na rundunar sojan saman Najeriyar, a fadin Air Vice Marshal Edward Gabkwet.

Ya ce sun samu bayanan sirri ne inda suka samu labarin yanbindigar na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen kamfanin doka da ke kusa da ƙaramar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

“Ƴan bindigar sun riƙa takatsantsan saboda suna tunanin ana bibiyarsu, inda daga bisani suka shige wani gida suka ɓoye, da rundunarmu ta ga haka sai aka kawai aka saki bom kan su.”

 

“Kuma mutum ɗaya bai tsira ba,” in ji Vice Marshal Gabkwet.

A cewarsa “Ƙaton bom muka jefa masu kuma ba mu samu labarin harin ya shafi farar hula ko mutum guda ba.”

Sai dai rundunar sojan saman ta Najeriyar ta ce ba ta samu cikakken bayanin sunayen ƴanbindigar da aka kashe ba.

“Sanin sunayen wadanda aka kashe yana daukar lokaci, kuma mutane sun fara goyon bayanmu sun gane cewa waɗannan ƴan bindigar idan aka bar su za su ci gaba da yin abin da suka ga dama, ” in ji Vice Marshal Edward Gabkwet.

Rundunar sojin saman ta bayyana cewa ba ta da labarin ko ayarin ƴanbindigar za su kai hari wani wuri ne.

“Abin da muka sani shi ne, ranar 28 ga watan Janairun, 2024, sun kai hari kan sojojinmu a Kwanar Mutuwa, kuma tun lokacin muke bibiyarsu, ” in ji Vice Marshal Gabkwet.

Najeriya dai na fama da matsalar tsaro a kusan sassan ƙasar, kuma duk ƙoƙarin jami’an tsaro amma kuma ƴanbindiga da ke satar mutane na ci gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso yammaci.

Share this Article
Posted by admin
Follow:
A group of seasoned crime reporters drawn from reputable media organisations in Nigeria. To help in creating a friendly Nigerian Police Force that meets the yearnings and aspirations of the citizens towards policing and security of lives and properties. To showcase the positive sides of the Force, as well as celebrating the great feat of police personnel, who have shown uncommon courage in the discharge of his / her responsibility. In the same vein, through objective ratiocination, identify the areas of shortcomings for corrections. We welcome you on board on this journey to build an enviable Nigeria Police Force by actively playing the role of a watch dog. Watch out for crime stories and other security titbits.
Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *