Maharan sun kutsa jami’ar ne da misalin karfe goma na dare inda suka shiga kasuwar da ke cikin jami’ar suna harbi a iska, abin da ya tayar da hankalin masu shaguna da sauran jama’ar da ke cikin kasuwar kuma kowa ya yi ta kansa.
Shugaban jami’ar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya ziyarci jami’ar a cikin daren Litinin domin kwantar da hankalin dalibai, ko da yake a cewar jami’ar ba ‘yan bindiga masu satar mutane ba ne, barayi ne kawai suka zo satar abinci a kasuwar dake cikin jami’ar. Tuni dai jami’ar ta dauki matakan kara karfafa tsaro a cikin wurin.
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sokoto a fannin tsaro Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya ya tabbatar da wannan harin, sai dai ya ce dabarun ‘yan bindiga na saka shakku da firgita a zukatan jama’a ne, saboda sun ga an tasar musu ta ko’ina.
A cewarsa matakan tsaron da ake daukao ba abu ne da ake bayyana wa a bainar jama’a ba, amma dai gwamnati tana kan daukar matakai don kawar da kalubalen.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da addabar jama’a a sassan Najeriya, don ko a makon nan rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kisan mutum uku da kuma raunata wasu mutane a wani hari da ya haddasa tashin hankali tsakanin al’ummomi biyu a yankin karamar hukumar Binji, kamar yadda kakakin rundunar a Sokoto ASP Ahmad Rufa’i ya tabbatar.
Mahukunta dai na cewa suna daukar matakai kuma ana ganin nasara ga wasu matakan da ake dauka na dakushe ayyukan ‘yan bindiga.
VOA




