Sheikh Giro Argungu Babban Abin Koyi Ne

Posted admin Arewa & Kai 659 Views 2 Min Read
2 Min Read

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya bayyana rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu a matsayin babban rashi  ga al’ummar Musumlin duniya baki daya.

Gwamnan ya kadu da jin rasuwar Sheikh Giro Argungu, wanda bayyana a masayin malami abin koyi da yake yada fatawa ta hanyar sunnar Annabi Muhammad (SAW) ba tare da jawo fitina ba.

“Rayuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu abun koyi ce domin ya sadaukar da kan sa wajen koyar da addini Islama da Kuma koyar da hakuri da wanzar da zaman lafiya.” Inji gwamnan.

Da yake mika ta’aziyyarsa da ma daukacin al’ummar Jihar Gombe ga iyalan Sheikh Giro, Gwamnan Inuwa, ya ce yaba da gagarumar gudummawar shehin malamin wajen yada da’awar Musulunci, wanda ya ce rasuwarsa ta haifar da wawakeken gibi mai wuyar cikewa a bangaren.

Inuwa wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, ya kuma jajanta wa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) inda Sheik Giro Argungu ya bada gudumawa sosai wajen ci gaban addini.

Sakon ta’aziyar, dauke da sa hannun kakakin gidan gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya yi wa Gwamnatin Jihar Kebbi da daukacin al’ummar Musulmi jajen wannan babban rashi da kuma addu’ar Allah Ya sa Aljanna ce makoma a gare shi.

Marigayi Sheik Abubakar Giro Argungu an shirya za a masa sallar jana’iza ne da misalin karfe 2 na rana a Babban Masallacin Idi na garin Birnin Kebbi.

 

Daily Trust

Share this Article
Posted by admin
Follow:
A group of seasoned crime reporters drawn from reputable media organisations in Nigeria. To help in creating a friendly Nigerian Police Force that meets the yearnings and aspirations of the citizens towards policing and security of lives and properties. To showcase the positive sides of the Force, as well as celebrating the great feat of police personnel, who have shown uncommon courage in the discharge of his / her responsibility. In the same vein, through objective ratiocination, identify the areas of shortcomings for corrections. We welcome you on board on this journey to build an enviable Nigeria Police Force by actively playing the role of a watch dog. Watch out for crime stories and other security titbits.
Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *